BBC navigation

Yawan wadanda suka mutu a gobarar Pakistan na karuwa

An sabunta: 12 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 14:27 GMT
Kamfanin kayan sawa na Karachi na ci da wuta

Kamfanin kayan sawa na Karachi na ci da wuta

A kalla kimanin mutane 246 ne suka mutu a sanadiyyar gobara a wata masana'anta a birnin Karachi a Kasar Pakistan.

Jami'ai sun ce wannan ita ce gobara mafi muni da aka taba samu ta masana'antu.

Mutane da dama sun samu raunuka, sakamakon gobarar da ta shafe kusan sa'oi 15 tana ci a cikin daren jiya.

Daruruwan mutane ne suka kasa fita daga masana'antar wacce ke da karafa a kewaye da ita.

Yawancin ma'aikatan sun durgo ne daga benen masana'antar.

Ana dai bukatar motocin kashe gobara arba'in da za su taimaka wajen kashe wutar.

Jami'an agaji dai sun shafe sa'oi da dama suna nemo gawawwakin mutanen da gobarar ta rutsa da su.

Rahotanni sun ce yawanci mutane sun makale a cikin ginin, suna ta kiran 'yan uwa da abokan arziki ta wayar salula, yayin da wutar ke ci.

Gobarar ta tashi ne sa'oi kadan bayan samun wata gobarar a wani kamfanin takalma da ke Lahore wadda ta yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 25.

An fara binciken musabbabin gobarar biyu, amma rahotanni na cewa gobarar sun auku ne a sanadiyar matsalar injinan janareta.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.