BBC navigation

Malema ya yi jawabi ga sojojin Afirka ta Kudu

An sabunta: 12 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:08 GMT
Julius Malema

Julius Malema

Dan siyasar nan na Afrika ta Kudu mai yawan jawo ce-ce-ku-ce, Julius Malema, ya bukaci dakarun da ke da korafi su hada kai a cikin da'a domin su yi gwagwarmayar neman hakkinsu.

Mista Malema ya furta wadannan kalaman ne ga wani gungun sojojin da ke fuskantar tuhumar rashin da'a sakamakon zanga-zangar da suka yi a shekara ta 2009 a kan albashi da kuma yanayin aiki.

Gabanin jawabin nasa dai, a karo na farko tun bayan da aka kawo karshen mulkin nuna wariyar launin fata a Afirka ta Kudu a shekara ta 1994, an sanya sansanonin sojin kasar ta Afirka ta Kudu cikin shirin ko-ta-kwana.

Ministar Tsaron kasar, Nosiviwe Mapisa-Nqakula, ta gargadi Mista Malema cewa kada ya kuskura ya ingiza fitina a tsakanin dakarun—hakan a cewarta zai iya kawo koma-baya a ci gaban da aka samu a kasar.

“A wannan karon tabbas Mista Malema ya wuce gona da iri—ina jin burinsa shi ne ya haddasa fitina a tsakanin jama'a da gwamnati, bayan da ya riga ya bayyana bukatarsa tun a baya game da masana'antun hakar ma'adinai”, inji ta.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.