BBC navigation

Tashin hankali a wuraren hakar ma'adinan Afirka ta Kudu na kara bazuwa

An sabunta: 12 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:38 GMT
Ma'aikatan hakar ma'adinai a Afirka ta Kudu

Tashin hankali a wuraren hakar ma'adinai a Afirka ta Kudu

Tashin hankali na kara bazuwa a bangaren ma'adinai na kasar Afrika ta Kudu.

Yanzu haka dai an dakatar da aiki a ma'adanin Platinum na wasu Amurkawa.

Ma'aikatan kamfanin sun ce masu zanga zanga ne su ka yi masu barazana shi yasa su ka fice.

Dan siyasar Afrika ta Kudu, Julius Malema, a jiya Talata ya yi kira ga ma'aikatan ma'adinai a kasar, su kori shugabanninsu, saboda a cewar sa basa aiki yadda ya kamata.

A watan daya gabata ne yajin aiki a mahakar ma'aidinai a Marikana ta janyo tashin hankali, inda mutane fiye da 40 suka mutu, wanda yawancinsu 'yan sanda ne suka harbesu.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.