BBC navigation

Zanga-zangar kin jinin Amurka a Libya da Masar

An sabunta: 12 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:21 GMT

Wani mutum a kusa da ofishin jakadancin Amurkan da aka kona a Benghazi

Masu zanga-zanga a birnin Benghazi na kasar Libya, sun kona karamin ofishin jakadancin Amurka da ke birnin don nuna fushinsu game da wani fim da Amurka ta shirya wanda ya yi batanci ga addinin musulinci.

Amurka ta ce an kashe ma'aikacinta guda daya, yayin da guda kuma ya samu raunuka sanadiyar zanga-zangar.

Rahotanni sun ce wasu 'yan bindiga da ke da alaka da kungiyar Islama sun jefa gurneti a ofishin jakadancin kafin su bude wuta.

A Masar ma, dubban masu zanga-zanga ne suka taru a wajen ofishin jakadancin Amurka a birnin Alkahira don nuna fushinsu da fim din.

Sun shiga ofishin inda suka kona tutar Amurka, kana suka maye gurbinta da ta Masar.

Amurka dai ta yi Alla-wadai da wadannan hare-hare da aka kai kan ofisoshinta.

Ba za mu yarda ba

Wasu bangarori na fim din da aka sanya a shafin Internet na YouTube, sun nuna wani mutum a matsayin Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi wasallam, kuma hakan ya haramta a addinin Musulunci.

Daya daga cikin masu zanga-zangar ya ce, : 'Yan Libya ba sa son a yi batanci ga Annabinsu. Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi wasallam ba Osama Bin Laden ba ne. Shi ne mutumin da Allah ya fifita a kan kowa. Don haka dole su dakatar da wannan fim din''.

Kazalika, wani da ya yi zanga-zanga a Masar mai suna, Abdallah Ibrahim Mohammad, ya ce kafafen watsa labarai na bayar da rahotannin karya game da musulinci:

''Kowannenmu na son ya bayyana ra'ayinsa cewa ba za mu taba lamuncewa a yi batanci ga Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wasallam ba. Hakan ya sabawa 'yancin fadin albarkin baki a ko'ina. Kowa na samun damar fadin albarkacin bakinsa amma ban da musulmai. Ana nuna musulmai a matsayin 'yan ta'adda''

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.