BBC navigation

Hukumar makamashin Nukiliya ta Duniya ta yi tir da Iran

An sabunta: 13 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:44 GMT
Hedikwatar Hukumar makamashin Nukiliya a Vienna

Hedikwatar Hukumar makamashin Nukiliya a Vienna

Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, IAEA, ta amince da gagarumin rinjaye da wani kuduri da ya yi tir da kasar Iran saboda shirinta na nukiliya.

Kudurin dai, wanda manyan kasashe 6 da suka hada Rasha da China da kuma Amurka suka gabatar, ya nuna matukar damuwa ne da yadda Iran din ke gudanar da ayyukan inganta karfen Uranium.

Hakazalika kudurin ya yi kira ga kasar ta Iran da ba Hukumar ta IAEA, hadin kai ba tare da bata lokaci ba. Robert Wood shi ne wakilin Amurka a Hukumar ta IAEA:

Ya ce,"Fatan da na ke shi ne Iran ta yi amfani da wannan dama domin ganin an warware wannan takaddama ta hanyar Diplomasiyya.Za mu gani idan za su mayar da martani, amma ina fatan za su yi."

Kasar ta Iran dai ta dage kan cewa shirin ta na nukiliya, na zaman lafiya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.