BBC navigation

Amurka na binciken kisan jakadanta a Libya

An sabunta: 13 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 06:39 GMT

Wani sashen na Ofishin Jekadancin Amuka a Bemgazi bayan kai masa hari.

Jami'an Amurka sun ce gwamnati na bincike ko harin da aka kai ofishin jakadancinta dake birnin Benghazi a Libya an shirya shi ne ko kuma ya faru ne kwatsam.

An kashe jakadan Amurka da wasu Amurkawa uku da kuma wasu 'yan kasar ta Libya kimanin goma ranar Talata a cikin wani harin da masu zanga-zanga kan fitar da wani fim a Amurka da ya ci zarafin addini musulunci suka ka yi.

Jami'an Amurka sun bayyana harin a matsayin wanda ak shirya, abin da ya sa Amurka ke ganin cewa kungiyoyin mujahidai ne suka kai shi.

Jam'ian gwamnatin sun ce ga alama an tsara kai harin na Benghazi ne tun kafin fitowar fim din.

Kuma suna jin ga alamu wata kungiyar masu kishin addinin musulunci masu dauke da makamai a kasar wadda ake kira Ansarul-Sharia na da hannu a harin.

Janye Jami'ai daga Benghazi

Wani jami'in Amurka ya ce Washinton ta bayar da umarnin kwashe daukacin ma'aikatan Amurka daga Benghazi zuwa Tripoli kuma Amurka za ta rage yawan ma'aikatanta zuwa adadin da ake bukata kawai idan bukatar gaggawa ta taso.

Gwamnatin kasar ta Amurkar ta kuma bayar da umarnin aikewa da wasu jiragen ruwan yaki biyu, zuwa gabar tekun Libya kuma ta aike da sojoji hamsin domin tsare ofishin jekadancinta dake babban birnin kasar wato Tripoli.

Sai dai kuma ta yi gargadin cewa kada a dauki an tsara hare-haren ne domin su zo daidai da ranar cika shekaru goma sha daya da kai harin sha daya ga watan Satumba a Amurka.

Bazuwar zanga-zanga

Tashen hankulan da aka samu a biranen Benghazi da Alkahira sun nuna alamun bazuwa zuwa wasu kasashen musulmai.

'Yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye a kan masu zanga-zanga a fusace, a wajen Ofishin jakadancin Amurka dake Tunisia kuma wasu daruruwa sun hallara a gaban wani ofishin dake Sudan.

A Morroco ma wasu masu zanga-zangar sun kona tutocin Amurka tare da yin kalaman tsinuwa ga Amurka, kusa da ofishin jakadancinta dake Casablanca.

Wadannan hare-haren dai za su iya sauya goyon bayan da Amurka ke baiwa guguwar sauyin dake kadawa a kasashen Larabawa, wadda ta kifar da shugabanin masu bin tsarin da baruwansu da addini a kasashen Masar da Libya da kuma Tunisiya, kuma ta dora masu kishin musulunci a kan mulki.

Hakama kuma hare-haren za su iya yin tasiri kan zaben shugaban kasar Amurka a watan Nuwamba, wanda za a yi karawa ta kud-da-kud a cikinsa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.