BBC navigation

Ministocin kasashen dake amfani da kudin CFA sun yi taro a Nijar

An sabunta: 13 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:03 GMT
Shugabannin kasashen UEMOA

Shugabannin kasashen UEMOA

Kwamitin koli na ministocin kasashe mambobin kungiyar tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma masu amfani da kudin CFA UEMOA , ya yi wani taro a birnin Yamai na Nijar domin yin nazari a kan matsalar karancin abinci a yankin.

Taron, wanda shugaban kasar ta Nijar Alhaji Mahamadou Issoufou ya jagoranta a matsayinsa na shugaban kwamitin, ya hada da abokan arziki masu hannu da shuni.

An dai tattauna a kan barazanar da farin dango da ambaliyar ruwa ka iya yi ga sakamakon damunar bana a cikin wasu kasashen yankin irin su Nijar da Mali da Senegal.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.