BBC navigation

Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya gargadi Amurkawa dake kasar

An sabunta: 13 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:39 GMT
Tutar kasar Amurka

Tutar kasar Amurka

Ofishin jakadancin Amurka a Nigeriya ya gargadi Amurkawa game da yiyuwar barkewar tashin hankali a kasar.

Wannan ya biyo bayan tarzomar da aka yi a wasu kasashen Larabawa da suka hada da Libya da Masar da kuma Tunisia.

Tarzomar dai ta faru ne sakamakon wani fim da aka yi a Amurka, wanda ke batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).

Ko a jiya ma musulmi sun gudanar da zanga-zangar lumana a birnin Jos na jihar Pilato don yin Allah Waddai da fim din.

Tuni dai rundunar 'yan sandan Najeriyar ta umurci jami'anta da ke kasar baki daya da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.