BBC navigation

Ana fargabar samun karancin abinci a Sahel

An sabunta: 13 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:57 GMT

Taswirar kasashen yakin Sahel

Wani jami'in majalisar dinkin duniya dake kula da ayyukan agaji a yankin Sahel ya nuna fargabar fuskantar matsalar karancin abinci a yankin a wannan shekarar.

Jami'in yace farin dango da suka bulla a yankin suna iya haddasa karancin yabanyar amfanin goma a kasashen dake yankin na Sahel.

Kuma tuni ayarin farko na farin ya riga ya bayyana a kasashen Nijar da Mali, kuma akwai fargabar wani ayarin na tafe.

Da ma dai Majalisar Dinkin Duniyar ta yi shelar ware kudade sama da biliyan daya na dalar Amurka don tunkarar lamarin.

Majalisar dai na ganin barnar da farin za su yi za ta iya shafar mutane miliyan hamsin, lamarin zai iya zama irin sa mafi muni tun shakara ta 2005.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.