BBC navigation

Jama'a na cigaba da nuna fushin su a Kasashen larabawa

An sabunta: 13 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:00 GMT
Zanga Zanga a Kasashen Larabawa

Ana ci gaba da zanga zanga a Kasashen larabawa

Jama'a da dama na ci gaba da nuna fushinsu a kasashen labarawa game da wani fim din da aka ci zarafin Manzon Allah (S.A.W) a cikinsa.

A Kasar yemen, masu zanga-zanga sun kutsa kai ofishin jakadancin Amurka, inda su ka kona motoci, kafin jami'an tsaro su kora su ta hanyar amfani da harbin bindiga.

A Alkahira, babban birnin kasar Masar, an samu karin tashe-tashen hankula a gaban ofishin jakadancin Amurka.

Wasu masu zanga-zangar sun bukaci a kori jakadan Amurka da ke kasar.

'Yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye kan masu zanga-zangar da ke jifansu da duwatsu.

An kuma samu wasu karin zanga-zangar a Kasashen Tunisia da Morocco da Sudan da Mauritaniya da kuma Iran.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.