BBC navigation

Danye Mai: Anambra ta mayarda martani ga makwabtanta

An sabunta: 14 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:54 GMT

Wani wurin hakar danyen mai a Najeriya

Gwamnatin jihar Anambra ta Najeriya, tayi watsi da da'awar da wasu jihohi makwabtanta suke yi, cewa su ma suna da hakki ga yankin da aka fara hako danyen mai a jihar.

A watan jiya ne dai Shugaban Najeriyar Goodluck Jonathan ya ayyana jihar a zaman ta goma a arzikin mai a kasar bayan ganowa tare da soma hakar danyen man a yankin Otu Oguleri.

Sai dai makwabtan jihohin Enugu da Kogi da kuma kungiyoyin wasu al'ummomi na jihohin biyu, sun ce suma suna da hakki ga yankinda ake hakar man don haka suke neman a kula da hakkokinsu a can.

A cikin wani jawabi ta kafafen watsa labarai gwamnan jihar Mr. Peter Obi ya bayyana mamaki ga yadda yace a duk tsawon shekarun da aka kwashe ana shirye-shiryen soma hakar danyen mai a yankin, babu wata jiha ko kungiyar da ta kalubalanci jihar ta Anambra game da mallakar yankin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.