BBC navigation

An kai hari kan Ofisoshin Jakadancin kasashen yamma a Sudan da Tunisia

An sabunta: 14 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:52 GMT

Cincirindon mutane cikin fushi sun kai hari kan Ofisoshin jakadancin Kasashen Burtaniya da Jamus a Sudan game da wani bidiyo da aka shirya a Kasar Amurka wanda ake masa kallon cin mutunci ne ga addinin islama.

Sun farfasa tagogi, tare da kuma cunna wuta a kan ofishin jakadancin Kasar ta Jamus

Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta ce babu abinda ya sami ma'iakatan ofishin jakadancin nata.

Haka kuma an gudanar da zanga zanga a Kasashen Yemen da Libya da Gaza da Afghanistan da Iraki da Malaysia dama Indonesia.

A lokacin hudubar Sallar jumaa, Limaman masallatai a birnin na Alkahira sun yi Allah Wadai da fim din ..

Sai dai sun yi kira ga jama'a da su yi zanga-zangar lumana, ba tare da tada hankali ba.

Bayan Sallar, dubban yan Masar sun taru a gaban Masallatai domin gudanar da zanga-zanga.

Sai dai wasu sun yi kokarin afka ma Ofishin jakadancin Amurka, amma jami'an tsaro suka tarwatsa su da barkonon tsohuwa suka koma dandalin Tahrir.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.