BBC navigation

Mujallar Faransa ta fusata Yarima William

An sabunta: 14 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:56 GMT
Kate Middleton

Maidakin Yarima William, Kate Middleton

Jami'an Gidan Sarautar Birtaniya sun ce Yarima William—wanda shi ne na biyu a layin masu jiran gadon sarautar—da maidakinsa, Kate Middleton, sun fusata da wadansu hotuna da wata mujallar Faransa ta wallafa, suna nuna Kate din kirjinta a bude.

Jami'an sun ce babu adalci a yadda aka yi katsalandan cikin harkokin rayuwarta ta sirri.

Yanzu haka dai ma’auratan biyu na neman shawara daga lauyoyi a kasar ta Faransa.

An dai dauki hotunan ne a lokacin da William da Kate suke hutu a kasar.

Tuni dai wadansu ’yan kasar suka fara bayyana ra’ayoyinsu game da hotunan da mujallar ta wallafa.

Daya daga cikinsu cewa ta yi, “Mujallar na aikinta ne kawai, ba wani abu bane. Idan ba ta yi hakan ba, ai ba za a ga hotunan nata ba”.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.