BBC navigation

'Ba za mu yarda da haramtattun tarurruka ba'

An sabunta: 14 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:37 GMT
Mahaka ma'adinai na zanga-zanga

Mahaka ma'adinai a Afirka ta Kudu suna zanga-zanga

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta bayar da sanarwa cewa ba za ta lamuncewa abin da ta kira haramtattun tarurruka ba, a kokarin da take yi na kawo karshen jerin yajin aikin da ake yi a wuraren hakar ma'adinai a kasar.

Kiris ya rage wannan sanarwa ta zama dokar ta-baci.

Ministoci a karkashin jagorancin ministan shari'a Jeff Radebe sun shaida wa manema labarai a birnin Pretoria cewa daga yanzu gwamnati ba za ta amince da tarurruka babu izini ba da kuma yawo da muggan makamai.

Sun kuma ce gwamnati za ta fara kame masu zanga-zanga domin kawo karshen abin da suka kira haramtaccen yajin aikin da ake ci gaba da yi a bangaren hakar ma'adinai na kasar.

Ministan da ke kula da ayyukan ’yan sanda, Nathi Mthethwa, ya kara da cewa an dauki wannan matakin ne domin maido da doka da oda a kasar.

'Ba zai yiwu a ci gaba da rasa rai ba'

Ya kuma ce ba zai yiwu ba a ce an ci gaba da rasa rayuka bayan mutanen da suka rasa rayukansu a lokacin tashin hankalin da ya faru a mahakar ma'adinai ta Marikana.

Ya ce alhakin gwamnati ne ta tabbatar da tsaron lafiyar jama’a a kasar ta Afrika ta Kudu.

Da ya ke hannunka mai sanda ga korarren shugaban matasan jam'iyyar ANC mai mulki, Julius Malema, ministan shari'ar kasar ya ce duk wanda ya karya doka—ko wanene shi—to lallai za a hukunta shi.

Sai dai kuma ya ce matakan da gwamnatin ta dauka ba ayyana dokar ta-baci ba ne.

An dai bayar da wannan sanarwa ne bayan masu hakar ma’adinan sun yi watsi da tayin da kamfanin Lonmin yayi musu na su kawo karshen yajin aikin makwanni biyar da suke yi.

Ma’akatan dai sun dage cewa ba su amince da tayin albashin da kamfanin yake yi musu ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.