BBC navigation

Fim: Musulmi sun yi zanga-Zanga a Nijar

An sabunta: 15 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:53 GMT

muhammadou issoufou, shugaban Jamhuriyar Nijar

Musulmin Jamhuriyyar Nijer sun bi sahun takwarorin su na wasu kasashen duniya wajen nuna fushinsu kan Fim din nan na batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W)

A birnin Damagaram mutane sun yi zanga zanga, inda suka kai hari kan wani coci dake garin na Damagaram suka cinna masa wuta.

Hukumomin birnin ba wanda ya jikkata ko ya rasa ran sa a cikin harin amma jami'an tsaro sun cabke mutane da daama.

Hakama an gudanarda addu'oin tsinuwa ga Amurka da wadanda suka shirya fim din a wasu masallatai

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.