BBC navigation

An yiwa mai fim din batanci ga Islama tambayoyi

An sabunta: 16 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:42 GMT

Daya daga cikin wurarenda aka yi zanga-zangar a Masar

'yan sanda a Amurka sun yiwa mutumin da amsa cewar yana da hannu a shirya Fim din nan daya tunzura jama'a a kasashen musulmi tambayoyi a ranar assabar.

An dai yiwa Nakoula Basseley Nakoula tambayoyin ne domin sanin ko ya keta wasu sharudda je-ka-gyara-halinka da aka gidanya masa bayan gama zaman sarka na watanni 21 kan shirya wata zamba a banki ta kafar internet a shekara ta 2010.

Daga cikin abubuwanda aka haramta masa yi har da anfani da internet ba tare da izni ba da kuma amfani da sunan bugi.

Wakilinm BBC Alastair Leithead a Birnin Los Angeles yace Nakoula Basseley Nakoula, wani kirista bakifde dake jahar California ya dade ba a gan shi ya fito bainar jama'a ba.

Ba an kama shi ne ba

Ya dai fita daga gidansa ne ya lullube fuskarsa da malfa da kuma wani mayafi inda 'yan sanda suka saka shi cikin wata motarda ke jiransa.

''Da tsakar dare ya fita da kansa daga gidansa inda yaje ofishin 'yan sandan tarayya suka yi masa tambayoyi na tsawon rabin sa'a dangane da wani laifin zamba da ya aikata a baya wanda a kansa aka yimasa daurin talalar je-ka-gyara halinka.'' Inji Wakilin na BBC.

Mr. Nakoula dai ya fadawa 'yan jarida cewar yana da hannu a shirya fim din wanda aka saka wa suna ''Innocence of Muslims'', amma ya musanta cewar shine ke da sunan bogi na Sam Bacile wanda aka yi anfani dashi waje saka fim a shafin Youtube.

'yancin fadar albarkacin baki dai yana babban matsayi a tsarin mulkin Amurka, don haka duk da kasancewar anyi tir da fim din Amurkar kuma ya haddasa zanga-zanga a duniyar musulmi, ga alama wadanda suka shirya fim din ba su aikata wani laifi ba da ake iya hukumta su karkashin dokokin kasar.

Sai dai anyi wa wani mai suna Steve Klein wanda yace shine wanda yayi kwangilar tsara fim din barazanar kashe shi, abinda ya sanarwa hukumar binciken manyan laifukka ta FBI.

Yayinda wani mutum daga wata kungiyar kiristoci a Jahar ta California wanda shine ya nemi iznin nadar Fim din daga hukuma ya shiga boyo.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.