BBC navigation

Fim: An umarci Amurkawa da su bar Sudan, Tunisia

An sabunta: 16 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:11 GMT

Shugaban Amurka Barack Obama yana jawabi yayin da sakatariyar harkokin waje Hillary Clinton ke tsaye a gefensa.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta umarci ma'akata Amurkawa da aikinsu bai zama dole ba da sauran 'yan kasar ta Amurka da su bar kasar Sudan,bayan sake samun wani zagaye na biyu na zanga-zangar da fitar Fim din nan na batanci ga addinin Islama ya tayar.

Ma'aikatar harkokin wajen tace gwamnatin Sudan ta dauki wasu matakai na takaita aiyukkan wadanda ta kira 'kungiyoyin ta'adda' , amma kuma ''yan ta'addan' suna nan a fili kuma sun yi barazanar kai hari kan muradun kasashen yamma.

Hakama ma 'aikatar ta bayar da irin wannan umarnin ga Amurkawan da ke Tunisia na su bar kasar tare da yiwa wadanda zasu rage can gargadin yin matukar taka-tsan-tsan.

A ranar Jumu'a dai ne aka sake harar ofisoshin jekadancin Amurkar dake biranen Khartoum da Tunis a cikin zanga-zangar kin jin Amurkar da fitar fim din na cin zarafin addinin musulunci ta tayar.

Kazamar zanga-zanga

Jami'in wata asibiti a Tunis yace mutane 4 ne suka mutu wasu kuma 46 suka samu raunuka a cikin tarzomar inda masu zanga-zanga suka tsallaka bangayen ofishin suka cinnawa wasu motoci wuta kana suka wawashe wata makarantar Amurkawa da ke kusa.

A Khartoum kuwa inda dubban masu zanga-zanga suka yi kokarin afkawa ofishin mutane 2 sun mutu bayan da aka kai hari kan ofisoshin jekadancin Jamus da Burtaniya.

Gwamnatin Amurkar dai na ganin cewar zanga-zangar wani masomi ne na wata fitina da za ta iya dadewa bata kwanta ba.

A yanzu gwamnatin ta Obama na kokakin takaita barnar suna da ta kadarorin da lamarin ya janyo mata inda take kokarin nisanta kanta daga ra'ayin da aka baiyana a cikin fim din a duk wata damar da ta samu.

A cikin jawabin da yake kowane mako ta gidan radiyo Mr. ya baiyana cewar Amurka na girmama mabiya kowane addini kwarai da gaske.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.