BBC navigation

Sabuwar takaddama tsakanin China da Japan

An sabunta: 18 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:22 GMT
Zanga-zangar China da Japan

Zanga0zangar China da Japan

Ana ci gaba da sainsa tsakanin kasashen China da Japan, bayan da sabuwar zanga-zanga ta sake barkewa a kasar China, game da tsibiran nan masu cike da takaddama

Dubun dubatar masu zanga-zangar ne suka hallara a wajen ofishin huldar jakadancin kasar Japan a birnin Beijing tare da 'yan sandan lura da yadda zanga-zangar ke gudana a kan titina, suna rera take suna kuma jefa kwalaben roba kan ginin.

Wannan ya biyo bayan zanga-zangar da aka gudanar a karshen mako kan harkokin kasuwancin kasar Japan kamar su kamfanonin lataroni na Panasonic da Canon, wadanda suka rufe harkokin gudanar da ayyukan wasu masana'antunsu.

A ranar 18 ga watan Satumbar 1931 ne sojojin Japan suka tarwatsa titin dogo da ke birnin Manchuria, kana suka dora alhakin kan masu bore.

Yayin da dai rikicin ya kara ta'azzara, yanzu haka Sakataren harkokin tsaron Amurka, Leon Panetta ya isa birnin Beijing domin tattaunawa da takwaransa da kuma manyan jami'an gwamnatin kasar ta China.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.