BBC navigation

An dauki faifen bidiyo a asirce na dan takarar jam'iyar Republican.

An sabunta: 18 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:28 GMT
Shugaba Obama da Mitt Romney

Shugaba Obama da Mitt Romney na kalubalantar juna

An dauki wani faifen bidiyo a asirce na dan takarar jam'iyar Republican a zaben shugaban kasar Amurka Mitt Romney, yana furta wasu munanan kalamai akan masu kada kuri'a 'yan Jam'iyar Democrat a wani taro na masu bada gudummuwa ga Jam'iyarsa da aka gudanar a farkon wannan shekarar.

Ya ce akwai kashi 47 cikin 100 na mutanen da za su zabi wannan shugaban ko ta halin kaka, su ne wadanda suka dogara da gwamnatinsa, suka kuma yi amannar cewa basu da zabi, kuma hakkin gwamnati ne ta kula da su, ta samar musu da kiwon lafiya da abinci da gidaje da dai sauransu, wadannan mutane ne dai basa biyan haraji kana kuma suna zaune ne hannu baka hannu kwarya.

Tuni dai ofishin yakin neman zaben shugaba Obama ya bayyana cewa zai yi wahala ga mutumin da bai dauki kusan rabin Amurkawa da muhimmanci ba ya iya jagorantar kasar, sai dai a martanin da ya mayar kan faifen bidiyon, Mr Romney ya ce duk da cewa ba'a fahimci kalamansa ba kamar yadda ya kamata amma yana nan akan bakansa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.