BBC navigation

Ma'aikatan Ma'adinai za su koma aiki a Afrika ta Kudu

An sabunta: 18 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:09 GMT
miners

Ma'aikatan ma'adinai a Afrika ta Kudu lokacin zanga zanga

Ma'aikatan mahakar ma'adinai ta Marikana a Afrika ta Kudu, za su koma aiki ranar Alhamis, lamarin da zai kawo karshen tashin hankalin da aka kwashe makonni shidda ana yi.

An ce yarjejeniyar da aka cimma da kamfanin, Lomnin, ta hada da karin albashi na kashi ashirin da biyu cikin dari.

Daya daga cikin wakilan ma'aikatan ya shaidawa BBC cewar karkashin yarjejeniyar, ba za a sauya wa ma'aikatan wuraren aiki ba, kuma babu korar ma'aikata.

Ma'aikatan sun rika shewa lokacin da suka ji batun karin.

Sun dai ki amincewa da tayin farko da aka yi masu, suna cewa cin fuska ne.

A watan Agusta 'yan sanda sun bude wuta kan masu zanga zanga a mahakar ma'adinan, inda suka halaka ma'aikata talatin-da-hudu.

Ana cewa yajin aikin nasu ya haddasa ma bangaren hakar ma'adinai na Afrika ta kudu asarar sama da dala miliyan dari biyar.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.