BBC navigation

Al-Shabab sun musanta ficewarsu daga Kismayo a Somalia

An sabunta: 18 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:46 GMT
Taswirar kasar Somalia

Taswirar kasar Somalia

Mazauna yankin tashar jiragen ruwan Kismayo dake kasar Somalia sun shaida wa BBC cewa mayakan kungiyar 'yan tawaye masu rajin kare addinin Islaman na al-Shabab da ke rike da ikon birnin sun fara ficewa.

Dakarun kungiyar Hadin kan Afirka dake marawa gwamnatin kasar Somalia baya na dada kusantowa gabar tashar ruwan na Kismayo a cikin yan watanni.

A cewar mazauna Kismayon, 'yan kungiyar ta al-Shabaab sun kauracewa ofisoshin da suka mamaye, tare da rufe gidan rediyo dake garin, kana kuma an ga 'yan kungiyar na kwashe wasu kayayyaki da suka hada da manyan bindigogi suna ficewa dasu daga garin.

Mai magana da yawun kungiyar ta al-Shabab Mohammed Usman Arus, ya tsaya kai da fata cewa kungiyar na nan daram a birnin na Kismayo, inda kana ya yi watsi da rahoton da cewa wata farfagandar yaki ce kawai.

Ya ce '' Dakarun Kenya da na Somalia tuni suka koma inda suka fito. Mun hallaka sojojinsu fiye da dari, kana mun ci karfin su. Suna kimanin kilomita dari da hamsin, nesa da Kismayo. Mun harbo jiragen yaki masu saukar angulu biyu a tsakiyar yankin.''

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.