BBC navigation

Mutane 26 sun mutu a gobarar masana'anta a Mexico

An sabunta: 19 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:42 GMT
Gobarar Kamfanin Pemex a kasar Mexico

Gobarar kamfanin sarrafa iskar gas na Pemex a kasar Mexico

Akalla 26 ne suka mutu a gobarar da ta tashi bayan fashewar wani abu, a masana'antar sarrafa iskar gas a jihar Tamaulipas dake arewacin kasar Mexico.

Kamfanin Pemex ya ce gobarar ta tashi ne, a daya daga cikin wuraren da ake sarrafa iskar gas dake wajen Reynosa, kusa da kan iyakar kasar da Amurka, inda ma'aikatan kamfanin da dama suka samu raunuka.

Cikin 'yan mintoci da fashewar abin ne motocin daukar marasa lafiya suka isa wurin, suna kwashe ma'aikatan da suka jikkata zuwa asibitocin da ke birnin Reynosa.

Wannan wani hatsari ne mafi muni da ya taba faruwa a masana'antar kamfanin na Pemex, tun bayan fashewar da ta faru a kusa da birnin Puebla dake gabashin kasar cikin shekara ta 2010, inda kimanin mutane 27 suka hallaka.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.