BBC navigation

Yau za a fara jigilar maniyyata aikin Hajji a Najeriya

An sabunta: 19 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:49 GMT
Taswirar Najeriya

Taswirar Najeriya

A Najeriya, yau ne za'a kaddamar da fara jigilar maniyyata aikin Hajji daga Najeriyar zuwa kasar Saudiya domin aikin hajjin bana.

A shekarun baya dai an sha fuskantar matsaloli dangane da jigilar maniyyatan zuwa kasa mai tsarki, ko kuma wajen dawo da su bayan kammala aikin Hajji, matsalar da a wasu lokutan a kan dora wa kamfanonin jiragen sama.

Kamfanin MAX Air shi ne kamfanin da zai yi jigilar alhazai mafi yawa a bana, inda zai yi jigilar sama da mahajjata dubu 45.

Kamfanin na MAX Air ya ce akwai jirage a filin saukar jiragen sama dake Kano, wanda za a tura jihohin Katsina da Sakkwato da Adamawa da kuma babban birnin tarayyar Abuja domin fara kwasar maniyyatan zuwa kasa mai tsarki.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.