BBC navigation

An soke majalisar datijjai a Senegal

An sabunta: 19 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:05 GMT
senate

Majalisar Dattijan kasar Senegal

Majalisar dokokin Senegal ta soke majalisar dattawa, da kuma mukamin mataimakin shugaban kasa.

Wannan mataki zai sa a samu rarar dala miliyan goma sha biyar, wadanda za a kashe a kan wadanda ambaliyar ruwa ta yi ma barna.

Sai dai masu sukar lamirin matakin sun ce an dauke shi ne da nufin rage karfin 'yan adawa.

Galibin 'yan majalisar dattawan magoya bayan tsohon shugaban kasar ne, Abdoulaye Wade, wanda shugaba Macky Sall ya kayar a zaben watan Fabrairu.

'Yan majalisar dattawan, su dari da hamsin, sun ta fadi-tashin ganin ba a soke majalisar tasu ba, amma majalisar wakilai ta kada kuri'ar amincewa da matakin.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.