BBC navigation

Jirgi mai saukar ungulu ya fadi a kusa da birnin Damascus

An sabunta: 20 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:41 GMT
Jirgi mai saukar ungulu na subutowa a kasar Syria

Jirgi mai saukar ungulu na subutowa a kasar Syria

Wani jirgi mai saukar ungulu ya fadi a kusa da Damascus, babban birin kasar Syria.

Rahotanni daga gidan talabijin na kasar sun ce jirgin ya subuto kasa ne a Douma, dake wajen gabashin birnin Damascus.

A karshen watan Augusta ne 'yan tawaye suka ce sun harbo wani jirgi mai saukar ungulu a wajen birnin na Damascus.

Mahukuntan kasar Syria suna cigaba da amfani da jirage masu saukar ungulu da sauran jiragen yaki, a yunkurin murkushe boren da 'yan tawaye ke yi, wanda ya fara tun a bara.

Ana dai cigaba da gwabza fada a biranen Damascus da kuma Aleppo dake arewacin kasar tun ranar Laraba.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International, ta yi gargadin cewa yawan kai hare-hare ta sama na ba-gaira-ba-dalili na dada haifar da asarar rayukan fararen hula a yankin Idlib da Hama.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.