BBC navigation

Zanga-zangar garanbawul din tattalin arziki a India

An sabunta: 20 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:32 GMT
Zanga-zanga a kasar India

Masu zanga-zanga a kasar India

Jam'iyun adawa da kungiyoyin ma'aikata a kasar India sun yi kira da a gudanar da wata gagarumar zanga-zangar nuna adawa da shirin yin muhimmin garanbawul ga tattalin arziki, wanda gwamnatin kasar ta sanar a makon jiya.

Masu shirya zanga-zangar sun ce miliyoyin mutane ne ake sa ran za su fito domin gudanar da zanga-zangar domin nuna adawar tasu da wannan aniya ta gwamnatin kasar.

Kananan 'yan kasuwa, da kungiyoyin dillalai sun ce suna da ja game da wannan yunkuri, domin a bar manyan kantunan kayan masarufi na kasashen waje su fafata da bangaren saye sa sayarwa na kasar India.

Masu zanga-zangar kuma suna adawa da aniyar gwamnati na kara farshin man diesel da kuma iskar gas na girki.

Masu sharhi dai sun ce adadin yawan masu adawa da wannan yunkuri, ya zama babban kalubale ga mahukuntan kasar wajen aiwatar da sauye-sauyen.

Tuni dai daya daga cikin muhimman jam'iyun dake cikin gwamnatin hadin kan kasar suka yi watsi da wannan yunkuri.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.