BBC navigation

Najeriya: anyi zanga-zanga akan fim din batanci

An sabunta: 20 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:07 GMT

A Najeriya, dazu ne kungiyar 'yan uwa musulmi karkashin jagorancin Sheik Ibrahim El Zakazaky ta gudanar da wata zanga-zangar nuna rashin amincewa da fim din nan na batanci ga musulunci da aka shirya a Amurka.

Yayin zanga-zangar dai an kona mutum-mutumin shugaba Obama na Amurka, kuma anyi ta rera Allah-wadai da Amurka da Isra'ila.

Zanga--zangar da aka yi a Zaria, ta samu halarcin dubban mutane daga sassan Najeriya daban-daban.

Wannan batu dai ya haddasa tarzoma a kasashen musulmi da dama.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.