BBC navigation

Pakistan: anyi zanga zanga akan fim din batanci

An sabunta: 20 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:40 GMT

Hukumomi a Pakistan sun umurci sojoji da su lura da dubban masu zanga-zanga a Islamabad, babban birnin kasar, wadanda ke zanga-zangar nuna kyamar fim dinnan ne da aka yi a Amurka, wanda yayi batanci ga addinin Islama.

'Yan sanda sunyi amfani da borkonon tsohuwa da burussai, don tarwatsa wani babban taron dalibai, wadanda suka yi kokarin shiga yankin da ake tsaro sosai na 'yan diplomasiyya, inda yawancin ofisoshin jakadancin kasashen yammacin Turai suke.

Hotunan telebijin sun nuna masu zanga-zanga a fusace suna aringama da 'yan sanda. Rahotanni sunce anjima kusan mutane 12 raunuka.

Wannan batu dai ya haddasa mummunar zanga-zanga kasashen musulmi da dama.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.