BBC navigation

'Yan gudun hijira na cikin mummunan hali a Sudan ta Kudu - Oxfam

An sabunta: 21 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:36 GMT

Sansanin 'yan gudun hijira a Sudan

Hukumomin Agaji na duniya sun ce suna cikin damuwa kan yadda halin take a sansanonin 'yan gudun hijira da suka kunshi fiye da mutane 100,000 a Sudan ta Kudu.

Kungiyoyin sun ce babban abin da ya fi sha damunsu shi ne rashin tsaftataccen ruwan sha a sansanonin.

Shugaban ayarin kungiyar Red Cross da ke ziyarar sansanin Yusuf Batil ya ce dole ta sanya mutane suke shan gurbataccen ruwan da ke kwance a kasa abin da ke sanya yara cikin hadarin kamuwa da cututtuka kamar na amai da gudawa.

Wata kungiyar bayar da agajin kuma ta Burtaniya, Oxfam, ta bayyana sansanonin da ke jihar Upper Nile a matsayin wani bam da ke jiran lokacin fashewa, watau ana dab da barkewar wata babbar annobar cuta.

Kakakin kungiyar, Alun McDonald, ya shaida wa BBC cewa akalla mutane 16 suka mutu sanadiyar kamuwa da cutar Hepatitis E.

Ya kara da cewa ana sa-rai yanayi a sansanoni zai kara dagulewa a watanni masu zuwa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.