BBC navigation

Ana kwaso 'yan gudun hijirar Habasha dake Yemen zuwa gida

An sabunta: 21 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 17:04 GMT
Sansanin 'yan gudun hijira na Dollo Ado

Ana kwaso 'Yan gudun hijirar Habasha dake Yemen

Ana kwaso 'yan gudun Hijira 'yar kasar Habasha dake Yemen zuwa babban birnin kasar Habashan na Addis Ababa.

Kungiyar da ke kula da masu gudun hijira ta kasa da kasa ta ce an kwaso 'yan gudun hijira 'yan kasar Habashan fiye da 500 a wannan makon, yayinda ake saran kwaso wasu 300 a mako mai zuwa.

Kungiyar tace 'yan gudun hijirar na daga cikin 'yar kasar Habasha dubu hudu dake zaune a budadden waje a arewa maso yammacin Yemen, wanda su ka kasa samun damar shiga cikin kasar Saudi Arabiya inda suke fatan samun aikin yi

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.