BBC navigation

'Yansandan kwantar da tarzoma sun kafsa da masu zanga-zanga a Girka

An sabunta: 26 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:13 GMT
'Yansandar kwantar da tarzoma na Girka

'Yansandar kwantar da tarzoma na Girka

Mummunar hatsaniya ta barke a wajen majalisar dokokin kasar Girka tsakanin 'yan sandan kwantar da tarzoma da masu zanga-zanga dake nuna bacin ransu kan tsuke bakin aljihun gwamnati.

'Yansandan sun yi amfani da hayaki maisa kwalla kan wasu daga cikin dubban masu zanga-zangar dake jifansu da duwatsu da kwalaben petur a tsakiyar birnin Athens.

Dayawa daga cikin masu zanga zangar sun shiga yajin aiki na tsawon sa'o'i 24 -- wanda shi ne na farko tun da gwamnatin Pirayin Minista, Antonis Samaras ta masu ra'ayin rikau ta hau kan karagar mulki a watan Yuni.

Wakilin BBC a Athens ya ce, komai a kasar ya tsaya cik, yayin da likitoci da malaman makaranta da sauran ma'aikata su shiga yajin aiki kan kara rage kudaden da gwamnati ke kashewaa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.