BBC navigation

Arik Air zai ci gaba da zirga-zirga a Najeriya

An sabunta: 23 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:09 GMT

Jirgin kamfanin Arik

A Najeriya, kamfanin jiragen sama na Arik Air ya ce daga ranar Lahadi zai koma zirga-zirgarsa a kasar bayan ya warware takaddamar da ke tsakaninsa da gwamnati.

Jami'an kamfanin sun ce sun dawo da zirga-zirgar ne bayan hukumomin sun gindaya musu sharuda a kan yadda ya kamata su rika tafiyar da lamuransu.

Kakakin kamfanin, Kaftin Ado Sanusi, ya ce a shirye suke su yi biyayya ga matakan da gwamnati ta sanya musu.

Ya bai wa masu hulda da kamfanin hakuri saboda matsalar da aka samu.

A makon jiya ne hukumar jiragen sama ta kasar ta dakatar da kamfanin daga zirga-zirga bayan ta zarge shi da gaza biyan kudin da take bin sa, duk da yake kamfanin ya musanta hakan.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.