BBC navigation

Kano: an yi zanga zanga akan fim din batanci ga musulunci

An sabunta: 22 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:09 GMT

Zanga-zanga a Kano

Dubun dubatar jama'a sun gudanar da machi a titunan birnin Kano dake arewacin Najeriya, domin yin zanga zangar kin jinin bidiyon nan da aka shirya a Amurka, wanda kuma ke yin batanci ga Manzon Allah SAW.

Wakilin BBC a arewacin Najeriya yace masu zanga zangar sun dauki tutocin Kasashen Amurka da Israi'ila, su kai ta jansu akan kasa.

Tutocin kuma na dauke da rubutun suka ga Shugaba Obama inda ake bayyana shi a matsayin dan ta'adda

An dai gudanar da zanga zangar cikin lumana

'Yan sandan kwantar da tarzoma sun rika bin masu zangar zangar har ya zuwa lokacin da aka kammala ta

Fim din dake nuna batancin ga Manzan Allah da kuma zane zanen batanci da wata jaridar Faransa ta wallafa akan Annabi Muhammadu ya janyo mummunan tashin hankali a kasashen duniya da dama

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.