BBC navigation

Fim:Lada ga wanda ya kashe mutumin da ya yi batanci ga musulinci

An sabunta: 23 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:12 GMT
Za a bayar da lada mai tsoka

Ghulam Ahmed Bilour

Wani Minista na gwamnatin Pakistan ya yi tayin ba da lada na tsabar kudi dala 100,000 ga duk wanda ya kashe mutumin da ya yi fim din da ya yi batanci ga addinin musulunci.

Ghulam Ahmed Bilour, wanda shi ne ministan harkokin jiragen kasa a gwamnatin hadin-gwiwa ta kasar, ya ce ya yi kiran ne don nunawa masu cin zarafin addinin musulinci cewa ba za su zauna lafiya.

Ya ce, " Zan biya duk wanda ya kashe wadanda suka shirya wannan fim dala dubu dari daya."

Ahmed Bilour ya yi kira ga kungiyoyin Taliban da al-Qaeda su shiga abin da ya kira aikin Allah.

Jam'iyarsa, ANP, wacce ke cikin gamayyar jam'iyun da suka kafa gwamnati ta nesanta kanta daga kalaman ministan.

Sai dai ta ce ba za ta dauki wani mataki ba.

Wani mai magana da yawun Firayim Ministan kasar ya shaida wa BBC cewa ba su da hannu a kalaman na Mista Bilour.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.