BBC navigation

Majalisar Dattawa ta yi barazanar tsige shugaban Najeriya

An sabunta: 22 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:22 GMT

Goodluck Jonathan

A Najeriya, Majalisar Dattawan kasar ta bi sahun Majalisar Wakilai wajen nuna yatsa ga bangaren zartarwa sakamakon rashin aiwatar da kudurce-kudurcen da Majalisun Dokokin kasar ke zartarwa.

Wasu daga cikin 'yan Majalisar Dattawan har barazanar tsige shugaban kasar suka yi idan bai sauya hali ba.

Sanata Uche Chukumerije ya ce shugaban kasar na da dabi'ar yin watsi da duk wani kuduri da 'yan majalisar suka amince da shi.

Ya ce: ''Idan batu ake yi na cire shugaban kasa, ai kowa ya san Uche Chukumerije ba a baya yake ba''.

Majalisar Dattawan dai ta ce ta dade tana hakuri da shugaban kasar saboda rashin aiwatar da kudurce-kudurcen da ta zartar ne saboda dattakunta.

Sai dai a cewarta daga yanzu za ta daina hakuri saboda ta ga alama shugaban ba shi da niyyar gyara halinsa.

A kan haka ne ma 'yan Majalisar Dattawan suka bai wa shugaban kasar wa'adin makonni biyu domin ya cire shugabar hukumar da ke sanya ido a kasuwar shunkun kasar, Misis Arunma Oteh, saboda zargin da ake yi mata na almundahana, idan kuma ya ki za su sanya wando daya da shi.

Sanata Ibrahim Musa ya shaidawa BBC cewa: '' Fadar shugaban kasa tana raina majalisa; akwai kudurce-kudurce da yawa da muka yi amma ba a aiwatarwa. Mun yi hakuri amma muna ganin hakurin ya kai karshe don haka a shirye muke mu yi duk abin da ya kamata a kan su''.

A baya dai ana zargin 'yan majalisar dattawan da zama 'yan amshin-shatan bangaren zartarwa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.