BBC navigation

An kashe dan majalisa a Somalia

An sabunta: 23 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:11 GMT

Shugaban Somalia Hassan Sheikh Mahmud

Wasu mahara a Mogadishu babban birnin Somalia sun harbe wani dan majalisar dokokin kasar Mustafa Hajj Mohammed.

Shi ne dan majalisa na farko da aka kai wa hari tun bayan sake zaben majalisar dokoki a watan Augusta bayan shafe shekaru ashirin babu majalisa a kasar.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce an yi masa harbi da dama ne a yayin da yake fitowa daga wani masallaci.

A makon jiya ma, wasu 'yan kunar-bakin-wake sun tayar da bama-bamai a Mogadishu inda suka kashe kansu da akalla mutane goma sha hudu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.