BBC navigation

Bauchi: Harin kunar bakin wake ya hallaka mutane uku

An sabunta: 23 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 13:56 GMT
Nigeria church attack

Wata mota da aka yi amfani da ita a wani harin kurnar bakin wake da aka kaiwa wata majami'a

A Najeriya, wani dan kunar bakin wake ya kaddamar da hari a kofar wata majami’a dake kan titin Wunti a cikin garin Bauchi dake arewacin kasar dazu, inda mutane uku suka hallaka yayin da wasu kusan hamsin suka jikkata.

Bayanai sun ce, lamarin ya faru ne yayin da dimbin mahalarta majami’ar St Johns ta Cathlic ke kokarin fitowa daga cikinta bayan kammala ibadar safiya, kuma a lokacin ne dan kunar bakin waken tuko mota daki mashigar majami’ar, kuma sannan ne bam din ya tarwatse amma bai yi lahani ga ginin majami’ar ba.

Kakakin rundunar 'yan sandan a jihar ta Bauchi, ASP Hassan Muhammd Auyo, ya shaidawa BBC cewa mutane uku ne suka rasa rayukansu ciki har da maharin yayin da wasu mutum arba'in da shida suka jikkata ciki har da 'yan sanda biyu.

Kungiyar agaji ta Red Cross a jihar ta Bauchi tare da hadin gwiwar hukumomi sun garzaya da wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibiti.

Shugaban kungiyar mabiya addini kirista ta Nijeriya wato CAN a jihar ta Bauchi, Rev Lawi Pokti, yayi Allah wadai da harin kuma yayi kira ga kiristoci akan kada su dauki fansa.

Kawo yanzu babu dai wanda ya dauki alhakin kai harin kuma ba a kai ga tantance maharin ba.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.