BBC navigation

Ambaliyar ruwa ta yi barna a Kogi

An sabunta: 24 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:53 GMT

Wani waje da ambaliyar ruwa ta lalata a Najeriya

A Najeriya, wata mummunar ambaliyar ruwa da ta aukawa jihar Kogi ta mamaye kananan hukumomi tara.

Ambaliyar, wace ta faru a sanadiyar bude madatsun ruwan Jebba da Shiroro da Ladoja na kasar Kamaru, ta shafe gonakin mutanen jihar ta Kogi da gidaje masu dimbin yawa.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA ta ce ya zuwa yanzu ba a samu rahoton asarar rayuka ba, amma ta ce dubban mutanen yankin suna cikin wani halin kaka-ni-ka-yi.

Jami'an hukumar sun ce ana cigaba da aikin ceto, kuma za a kai wa mutanen da lamarin ya shafa kayayyakin bukatu na yau-da-kullum.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.