BBC navigation

Za a ci gaba da tattaunawa tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu

An sabunta: 24 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:23 GMT
An dage tattaunawa tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu

Shugaban Sudan da na Sudan ta Kudu

A ranar Litinin ne shugabannin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu za su ci gaba da tattaunawa game da rashin jituwar da ta kusa kai su yaki a farkon shekarar nan.

Muhimman batutuwan da tattaunawar ta keke-da-keke za ta maida hankali sun hada da sha'anin tsaron bakin iyakokin kasashen.

Yadda za a raba kudaden da ake samu ta hanyar fitar da man fetur da kuma yankin Abyei da ake takaddama akai.

Shugabannin biyu dai na tattaunawar ce a Habasha.

An dage tattaunawar ce ranar Lahadi bayan shugabannin sun kwashe fiye da sa'oi biyu suna yin ta.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi barazanar sanyawa kasashen biyu takunkumi, idan ba su cimma wata kwakkwarar yarjejeniya ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.