BBC navigation

Ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu

An sabunta: 24 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:40 GMT
shugaba al Bashir na Sudan

shugaba al Bashir na Sudan

Ana ci gaba da wani muhimmin taron koli tsakanin shugaban kasar Sudan da na Sudan ta Kudu, a kasar Ethiopia, makwabciyarsu.

Kasashen biyu sun gwabza fada a kan iyakar da suke takaddama a kai, cikin watan Aprilu, kasa da shekara guda bayan da Sudan ta Kudu ta balle.

Ana taron kolin ne da nufin cinma wata cikakkiyar yarjejeniya kan batutuwa da dama, da suka hada da na man petur, da kuma kan iyaka.

Zaman farko na taron bai dauki wani dogon lokaci ba. Kasa da fara taron da sa'a guda na shugabannin kasashen biyu da masu shiga tsakani na kungiyar tarayyar Afrika da praministan Habasha, tawagogin suka koma masaukinsu.

Wani jami'in Sudan ya shaidawa BBC cewa, manyan masu shiga tsakanin za su gana don warware inda ake samun bambamce-bambamce.

Jami'an kasar Sudan din sun ce babban abun damuwa a tattaunawar shi ne batun ware tudun mun- tsira wanda fadinsa bai fi Mil goma sha hudu ba.

Haka kuma sauran batutuwan da ake tataunawa kan su a wajen taron sun hada da batun kan iyaka na Abyei da ake rikici a kansa da batun man petur, da kuma sauran iyakokin da ake takaddama a kansu.

Wani ministan a Sudan ya shaidawa BBC cewa, ana kokarin tsara yarjejeniyar filla-filla a taron. Dukkanin kasashen dai na fuskantar matsin lamba daga kasashen waje kan su cimma yarjejeniya guda mai ma'ana.

Majalisar dinkin Duniya dai ta yi barazanar sanyawa kasashen takunkumi muddin ba a cimma matsaya guda ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.