BBC navigation

Jirgin ruwa mai daukar jiragen sama ya fara aiki a China

An sabunta: 25 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:50 GMT
Jirgin ruwan daukar jiragen sama na kasar China

Jirgin ruwan daukar jirgen sama n kasar China na farko

Kasar China ta ce jirgin ruwanta mai daukar jiragen sama ya fara aiki a hukumance.

Jirgin ruwan mai suna Liaoning, tsohon na tarayyar Soviet ne wanda China ta siya daga kasar Ukraine a shekarar 1998 aka gyara shi sosai.

An sa masa sunan yankin arewa maso gabashin kasar ne inda birnin Dalian yake, wato birnin da sansanin sojin ruwan Sin yake.

Ma'aikatar tsaron China ta ce jirgin ruwan zai kara karfin China na kare 'yancinta na cin gashin kanta, da tsaronta.

Sai dai masu sharhi sun ce ba a tsammanin cewa jirgin ruwan zai fara daukar jiragen sama tukuna.

Samun jiragin ruwan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Japan da sauran kasashe da ke yankin ke nuna damuwarsu kan kara kasaita da karfin da Chinar ke samu a fannin harkokin sufurin ruwa.

Kasashen China da Japan dai na cikin halin sa-in-sa kan wasu tsibirai dake gasbashin tekun China, wadanda kasashen biyu ke ikirarin mallaka.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.