BBC navigation

An fara taron Majalisar Dinkin Duniya

An sabunta: 25 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:55 GMT
Ban Ki-moon, sakatare janar  majalisar Dinkin duniya

Ban Ki-moon, sakatare janar na Majalisar Dinkin duniya

An bude babban taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York.

Shugaba Obama ya fara jawabinsa ne da yaba ma jakadan Amurka a Libya, Chris Stevens, wanda aka kashe Benghazi a farkon watan nan.

Ya ce Amurka, ba zata huta ba, sai ta gano wadanda suka aikata kisan, an kuma hukunta su.

Shugaba Obama ya kuma nuna takaicinsa kan tashin hankalin dake faruwa, bayan abin da ya kira, hoton bidiyo, abin kyama da aka yi na batanci ga Manzon Allah , tsira da amincin Ala su Tabbata a gare shi.

Haka nan shugaba Obama ya bukaci a kawo karshen gwamnatin shugaba Assad a Syria.

A nasa jawabin, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniyar, Ban Ki -moon ya bayyana halin da ake ciki da cewa cike yake da rudani, da komawa tafarkin siyasa, da kuma sauye sauye.

Ya yi kira ga dukkan kasashe da su guji kalaman yaki, su rungumi na zaman lafiya, yana mai cewa nauyi ne da ya rataya a wuyan shugabanni, su tabbatar da wanzuwar zaman lafiya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.