BBC navigation

Kananan yara a Syria sun tagayyara- Save the Children

An sabunta: 25 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:56 GMT
Kanan yara a kasar Syria

Kanan yara a kasar Syria

Kungiyar kare hakkin yara ta Save the Children, ta wallafa bayanai na ban ta'ajibi game halin kuncin da kananan yaran da suka gudu daga kasar Syria suka shiga na cin zarafi da azabtarwa.

Yaran sun bayyana halin kunci, azabtarwa da cin zarafin da suka samu kansu a ciki yayinda suke tsare a kasar ta Syria.

Kungiyar Save the Children din kuma ta ce kusan ko wane yaro cikin yaran da suka yi kokarin iya ficewa daga kasar Syria da ta yi magana da su ya ce ya ganewa idanunsa yadda aka kashe iyalansa.

Wani yaro mai kimanin shekaru goma sha biyar wanda duk jikinsa ke cike da tabon kunar wutar taba sigari, ya ce wannan na cikin azabar da aka gana masa lokacin yana kurkuku da ya ce ya zama kamar makaranta a gareshi.

Wasu yaran kuma sun bayyana cewa an yi musu azaba da wutar lantarki, tare da hada su cikin kurkuku da gawawwakin da suka riga suka rube, yayinda wani a cikinsu ke cewa ya ganewa idanunsa yadda wani yaro mai kimanin shekaru 6 da haiuwa ya rasa ransa bayan da aka azabtar da shi kana aka daba masa wuka.

Tun daga watanni goma sha takwas din da aka shafe ana fama da tashe tashen hankula a kasar Syriar da ya kai ga cafkewa da azabtar da kananan yara a a birnin Darra, masu fafitika sun ce kimanin yara 2,000 aka hallaka, kana karin wasu da yawa sun samu kansu cikin halin dimuwa.

Kungiyar ta Save the Children ta ce tana shan ganin ta'asa da abubuwa marasa kyawun gani da basu misaltuwa.

Duk da cewa dai ba ta fito ta bayyana wane bangare ne ke da alhakin aikata ta'asar ba, amma kungiyar agajin ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta kara azama wajen daukar matakai masu tsauri, tare da hukunta wadanda suka aikata lafin na kisa, cin zarafi da azabtar da kananan yaran.

Wannan rahoto na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara gudanar da babban taron shekara na Majalisar Dinikin Duniya.

A baya dai manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniyar, Lakhdar Brahimi ya ce rikicin na kasar Syria ya kara kazancewa yana kuma kara ta'azzara ne.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.