BBC navigation

Tagwayen 'bama-bamai' sun girgiza Damascus

An sabunta: 26 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:45 GMT
Fashewar bom a Damascus babban birnin kasar Syria

Fashewar bom a Damascus babban birnin kasar Syria

Wasu manyan tagwayen abubuwa da suka fashe sun girgiza Damascus, babban birnin kasar Syria, kuma sun faru ne a kusa da gidajen jami'an sojin kasar.

Harin dai ya faru ne da misalin karfe bakwai na safiyar Laraba a wuraren da galibi gine-ginen gwamnati suka fi mamayewa.

Wakilin BBC a birnin ya bayar da rahoton jin karar fashewa da kuma hangen wuta na tashi daga yankin.

Kana daga bisani bakin hayaki ya turnuke sama daga gine-ginen da aka kaiwa harin, sai dai babu tabbaci kan musabbin abkuwar fashewar.

Gidan talabijin na kasar da helkwatar ta ke kusa da inda fashewar ta auku, ya bayyana musabbin abkuwar da cewa harin ta'addanci ne.

Shaidu sun ce fashewar ta biyu ta abkawa harabar babban ginin sojin kasar, yana kuma ci gaba da cin wuta.

Motocin daukar marasa lafiya sun yi ruguguwar kai dauki zuwa wurin da lamarin ya auku.

Yayin da ake bayar da rahoton samun jikkata da kuma ci gaba da musayar wuta tsakanin dakarun 'yan tawaye da na gwamnati.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.