BBC navigation

Yajin aikin gama-gari a kasar Girka

An sabunta: 26 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:53 GMT
Masu zanga-zanga a kasar Girka

Masu zanga-zanga kan tsuke bakin aljihu a kasar Girka

Kungiyoyin ma'aikata a kasar Girka na gudanar da yajin aikin gama gari na farko tun bayan kafuwar gwamnatin Firaminista Antonis Samaras, a cikin watan Yuni.

Wannan ya biyo bayan nuna adawarsu da yunkurin kara zaftare kudaden da gwamnatin ke kashewa da wajen sama da dala biliyan goma sha biyar.

Dubun dubatar jami'an 'yan sanda ne aka girke a tsakiyar birnin Athens, domin kiyaye yiwuwar barkewar tashin hankali, wanda ya sha faruwa a baya.

Ma'aikata daga sassan ma'aikatu da kamfanoni masu zaman kansu daban-daban ne da suka hada da likitoci, masu karbar haraji, malaman makarantu da masu shaguna suka shirya tsunduma cikin yajin aikin da zanga-zangar nuna adawa da wannan mataki na tsuke bakin aljihu.

Bayanai dai sun ce masu lura da zirga-zirgar jiragen sama su ma za su katse ayyukansu na rabin rana,wanda hakan zai iya kawo tsaiko kan harkokin yau da kullum a kasar ta Girka.

Da dama dai na fargabar yiwuwar a samu maimaituwar barkewar rikici sakamakon wannan yajin aiki da zanga-zangar a bisa titina.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Girka ke yunkurin sasantawa kan sabon tsarin zaftare kudaden da take kashewa da ya kai fiye da Euro biliayn 11, tare ta yunkurin kudaden pensho da kara yawan shekarun yin murabus zuwa shekaru 67.

Idan aka duba adadin yawam marasa aikin yi a kasar ta Girka dai, kana kuma adadin masu fama da kangin talauci, kasar ta sake fadawa cikin yanayin tsaka mai wuya.

Sakon masu zanga-zangar dai shi ne idan har gwamnatin kasar Girkar ta aiwatar da yunkuruinta, to al'amuran za su kara tabarbarewa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.