BBC navigation

Najeriya ta dakatar da jigilar mahajjata

An sabunta: 26 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 22:15 GMT
Dakin ka'aba

Ka'aba

Hukumar aikin Hajji ta Najeriya ta sanar da dakatar da jigilar maniyyatan kasar zuwa kasar Saudiyya har na tsawon kwanaki biyu.

Hukumar ta ce ta dauki wannan matakin ne don ganin an warware takaddamar da ta kaure tsakanin hukumomin kasar da na Saudiyya dangane da dawo da mahajjata mata 'yan Najeriya dari da saba'in da daya zuwa gida bisa hujjar cewa, matan ba sa tare da muharrramansu.

A ranar Laraba ne dai aka mayar da wasu alhazan Najeriya mata da Saudiyya ta hana su shiga kasar ta saboda rashin muharramai.

An mayar da matan ne dauke da maniyyata daga jihar Taraba a cikin wani jirgi da ya sauka a filin saukar jiragen sama na Mallam Aminu Kano, da ke birnin Kano a arewacin kasar.

Matan mahajjata dake tsare a hannun hukumomin Saudiyyar sun kusa kaiwa dubu guda.

Tun da farko hukumomin Najeriya sun ce suna daukar matakai na ganin an warware takaddamar da ake yi tsakanin hukumomin kasar Saudiya dangane da alhazan Najeriyar mata da ake tsare da su a filin jirgin Sarki Abdulaziz dake Jiddah.

Rahotanni sun ce yanzu haka dai alhazan mata da hukumomin Saudiya suka hana su shiga kasar domin aikin hajji, bisa zargin ba su je da muharramai ba, na cewa halin da suke ciki yana kara muni.

Bayanai daga Hukumar jin dadin Alhazai ta Najeriya na cewa ana tattaunawa tsakanin jami'an ofishin huldar jakadancin Najeriya da hukumomin kula da harkokin kasashen waje na kasar Saudi Arabia domin warware matsalar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.