BBC navigation

Obama ya yi Allah wadai da tsattsauran ra'ayi

An sabunta: 26 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:22 GMT
Zauren babban taron Majalisar Dinkin Duniya a Amurka

Zauren babban taron Majalisar Dinkin Duniya a Amurka

Shugaban Amurka Barack Obama ya yi amfani da jawabinsa ga babban taron Majalisar Dinkin Duniya wajen yin kira ga shugabannin kasashen duniya da su fito da babbar murya wajen yin Allah wadai da tashe-tashen hankula da ta'addanci, kana su hada kai da Majalisar Dinkin Duniya wajen gano tushen yawan fusata a fadin kasashen Musulmi.

Mr Obama ya yi kira da a kawo karshen gwamnatin shugaba Bashar Assad na kasar Syria, yana mai cewa makomar kasar ba za ta ci gaba da kasancewa karkashin mai mulkin kama karya wanda ke yiwa al'ummarsa kisan gilla ba.

Shugaba Obaman dai yayi amfani da dogon jawabinsa, wanda shi ne na karshe kafin zaben shugaban kasa da za a gudanar a Amurkar cikin watan Nuwamba, ga daukacin kasashen duniya wajen yin kira ga yin juriya da girmama al'adu da addinan juna, kana kuma ya ce Amurka za ta yi duk yadda za ta yi wajen hana kasar Iran mallakar makaman nuclear.

Mr Obaman ya kalubalanci kasashen duniya da su yi fito na fito da tushen hargitsin da ke faruwa a yankin Gabas ta tsakiya, inda ya ke kuma yin Allah wadai da kiyayyar da ta biyo bayan abinda ya kira mummuna kuma gurbataccen faifan bidiyon nan da ya haddasa fusata a fadin kasashen Musulmi, sai dai kuma ya yi Allah wadai da zanga-zanga da tashe-tashen hankulan da suka faru a wasu kasashen don nuna bacin ran da ya biyo bayan nuna faifan bidiyon.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.