BBC navigation

An gana tsakanin Congo da Rwanda a New York

An sabunta: 27 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:32 GMT
shugaba Kabila na Congo

shugaba Kabila na Congo

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban ki-Moon, ya kaddamar da saduwa tsakanin shugabannin kasashen Rwanda da Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, a wani kokarin kawo karshen rikicin kan iyakar kasashen.

Taron, wanda aka yi a bayan fage, an kammala shi tare da bayar da wata sanarwa, mai cewa kasashen biyu na mutunta ingancin fadin kasar da kowacensu keda ita.

Congo dai ta dade tana zargin Rwanda da laifin baiwa 'yan tawaye makamai da jami'ai a gabacin Congon.

A wata tattaunawar da yayi da BBC kafin taron, Shugaban Congon, Joseph Kabila ya ce yana ganin cewa za a iya warware matsalar a siyasance ko ta hanyar yaki.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta gabatar da wani sako mai karfi ga shugaba Kabila na Jamhuriyar Congo, da Paul Kagame na Rwanda cewar ya zama wajibi su samo hanyar warware wannan takadama.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.