BBC navigation

Saudiyya ta cigaba da mayar da maniyyatan Najeriya

An sabunta: 27 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 11:39 GMT
Wasu maniyyatan Najeriya a jihar Kano

Wasu maniyyatan Najeriya a jihar Kano

Hukumomin Najeriya na cigaba da mayar da maniyyatan Najeriya mata zuwa gida Najeriya bisa hujjar cewa, matan ba su je kasa mai tsarki da muharramai ba.

Kuma tuni gwamnatin Najeriya ta sanar da shirin aike wata tawaga zuwa Saudiyya domin yin tattaunawa akan wannan batu.

Kakakin majalisar wakilai, Hon. Aminu Tambuwal ne zai jagoranci tagawar da zata je Saudiyya.

Hukumar dai ta sanar da dakatar da jigilar maniyyatan kasar zuwa kasar Saudiyya har na tsawon sa'oi 48.

Hukumar ta ce ta dauki matakin ne don ganin an warware takaddamar da ta kaure tsakanin hukumomin Najeriya da na Saudiyyan dangane da dawo da mahajjata mata 171 gida.

Sauran 'yan tawagar sun hadar da karamin ministan harkokin wajen Najeriya, da shugaban hukumar alhazai ta kasar da kuma wasu malaman addinin Musulunci.

Haka kuma mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo ya baiwa Saudiyyar wa'adin sa'oi 24 a warware takaddamar, a wata ganawa da ya yi da jakadan Saudiyya a Najeriya, Khaled O.Y. Abdrabuh.

Koda dazu ma dai wasu mata mahajjan Najeriya da aka tuso keyarsu sun sauka a filin jiragen sama na Kano.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.