BBC navigation

Sudan da Sudan ta Kudu za su sa hannu a yarjejeniya

An sabunta: 27 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 09:10 GMT
Shugabannin Sudan da Sudan ta Kudu a lokacin tattaunawar

Shugabannin Sudan da Sudan ta Kudu a teburin tattaunawa

Kasashen Sudan da Sudan ta Kudu sun amince da wata yarjejeniyar da za ta bu su damar cigaba da jigilar mai daga kudanci zuwa arewaci don kaiwa kasashen ketare.

A yau ne ake sa ran shugabannin kasashen biyu za su rattaba hannu a kan wannan sabuwar yarjejeniyar.

Za kuma su rage sojojinsu dake kan iyakokinsu.

Bayan kwanaki hudu suna tattaunawa kan batutuwa da dama a kasar Habasha.

Sai dai akwai batutuwan da har yanzu ba a kai ga warware su ba, musamman ma dai batun takaddamar mallakar yankin Abyei.

A farkon wannan shekarar ce dai, takaddama tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu ta kusa jefa kasashen cikin yaki.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.